Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

A ranar Alhamis din da ta gabata ne mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya yi ganawa ta sa’o’i biyu da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo. Bayan kammala tattaunawar, Sarki Muhammadu Sanusi II bai bayyana wa manema labarai ziyarar mukaddashin shugaban kasar da kuma abubuwan da suka tattauna, sai dai Kamfanin dillancin labarai ta Najeriya NAN ta samo wannan dalilin ziyarar ta Sarki Sanusi daga majiya mai tushe. NAN ta bayyana cewa Sarki Sanusi ya yi kafa da kafa ne don ya jaddada godiyarsa ga Farfesa Osinbajo bisa saka baki da ya yi wajen tsayar da binciken masarautar Kano da majalisar dokokin jihar ta fara kan zargin masarautar da Sarki da wasu laifuka har guda 8, wanda daga ciki har da yin 'wa kaci ka tashi da dukiyar masarauta'. Read more: https://hausa.naij.com/1110535-dalilin-da-yasa-sarkin-kano-ya-kaiwa-mukaddashin-shugaban-kasa-osinbajo-ziya.html

LEAVE A COMMENT